Zanga-Zanga: Firaiministar Bangladesh Sheikh Hasina, ta yi Murabus

 

Firaiministar Bangladesh Sheikh Hasina, ta yi murabus sannan kuma ta bar kasar.

Rahotanni sun ce ta gudu ta bar kasar ne tare da ‘yar uwarta inda ta nufi kasar India.

Dubban masu zanga zanga ne suka afka ofishin firaiministar da ke Dhaka babban birnin kasar.

Sheikh Hasina, ta bar ofishin nata ne tun kafin masu zanga zangar su shiga ciki.

Wasu hotuna da kafar talbijin din kasar ta nuna sun nuna masu zanga zangar na shiga cikin ginin ofishin a fusace.

Rahotannin sun ce shugaban sojojin kasar zai tattauna da shugabannin jam’iyyun siyasa da kuma kungiyoyin fararen hula a kasar don kafa sabuwar gwamnati a kasar.

Tun da farko masu zanga zangar sun yi ta kira a kan ta Sauka.

A watan daya gabata ne aka fara zanga zanga a kasar saboda sabon tsarin rabon guraben aiki da gwamnati da bullo da shi abin da bai yi wa ‘yan kasar dadi ba musamman dalibai.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here