Ana Duba Yiwuwar Mayar da Makarantun Firamare da Sakandire Hannun Gwamnatin Tarayya
Majalisar dattawan Najeriya tana duba wani ƙudiri game da batun dubban yaran da ba sa zuwa makaranta a sassan ƙasar, da nufin gano matsalolin da ke hana su zuwa makaranta, tare da nemo hanyoyin magance su.
Read Also:
Ana kuma duba yiwuwar fito da wani tsari na bai-ɗaya da zai mayar da makarantun firamare da sakandare kacokan hannun gwamnatin tarayya, tare da sama masu kasafin kuɗi na mausamman.
Sanata Lawal Adamu Usman, wanda aka fi sani da Mista La, mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, kuma shugaban kwamitin ilimi a matakin farko na majalisar dattawan ne ya bayyana wa BBC haka.