Bayan Ayyana Dokar Ta-baci, Ina Gwamna Fubara ya Shiga ?
Rivers – Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ayyana dokar ta-baci a jihar Ribas da ke Kudu maso Kudancin Najeriya a daren Talata, 18 ga watan Maris, 2025.
Bola Tinubu ya sanar da wannan mataki ne yayin wani jawabi da ya yi wa ‘yan ƙasa kan halin da jihar Ribas ta tsinci kanta.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X.
A cewarsa, matakin ya zama dole domin dawo da doka da oda a jihar mai dumbin arzikin man fetur.
Bola Tinubu ya naɗa gwamnatin riko
Sanarwar ta kuma haɗa da dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara, mataimakiyarsa Ngozi Odu, da dukkan ‘yan majalisar dokokin jihar na tsawon watanni shida.
Shugaban ƙasa ya naɗa tsohon hafsan sojan ruwa, Vice Admiral Ibokette Ibas (mai ritaya), a matsayin wanda zai jagoranci al’amuran jihar.
Bayan ‘yan sa’o’i kaɗan da sanarwar, sojoji suka mamaye gidan gwamnati da ke birnin Fatakwal.
Ina Gwamna Fubara ya shiga?
Read Also:
Wani majiyar Punch ya bayyana cewa gwamnan na nan a gidansa da ke cikin fadar gwamnati lokacin da sojoji suka mamaye wurin da misalin ƙarfe 9:00 na dare.
“To, a halin da ake ciki yanzu, akwai sojoji a cikin gidan gwamnati amma gwamna ya na nan a gidansa da ke fadar gwamnati ya yi zamansa.”
Har ila yau, an girke wata motar sulƙe ta yaƙi (APC) a ƙofar shiga fadar gwamnati, tana kallon babban titin da ke gabanta.
Wani ɗan jarida da ya ziyarci wurin da misalin ƙarfe 9 na dare ya ga motocin alfarma (SUVs) da dama a gaban ƙofar gidan gwamnati, masu fitilu a kunne.
Sai dai Babu tabbacin ko gwamnan yana shirin barin gidan gwamnati ne ko akasin haka.
Halin da jama’a ke ciki a Fatakwal
A cikin birnin Fatakwal, an ga jama’a da direbobi na hanzarta komawa gidajensu bayan sun ji sanarwar ayyana dokar ta-baci.
Haka nan, mutane da yawa sun taru a kan tituna suna tattauna batun, inda wasu suka nuna damuwa da takaici game da lamarin, suna zargin ‘yan siyasa da haddasa rikicin da ya kai ga wannan mataki.