Jalingo: Bata Gari Sun Kai Farmaki Cibiyar Killace Masu Korona, Sun Yashe Komai
Fusatattun matasa sun kai mamaya cibiyar killace masu cutar korona a garin Jaligo
Sun sace gadaje, katifu da sauran kayayyakin da ke cibiyar – A yanzu haka an tattaro cewa cibiyar ta zama wayam babu komai a ciki Wasu da ake zaton bata gari ne sun kai farmaki cibiyar killace masu cutar korona a Jalingo, babbar birnin jihar Taraba, sannan suka tafi da katifu da sauran kayayyakin da ke cibiyar. Dubban matasa ne suka kai wa cibiyar wanda ke a sansanin NYCS, hanyar Wukari – Jalingo farmaki, inda suka fasa kofofin cibiyar. An tattaro cewa yan iskan sun sace dukkanin katifu kimanin guda 200 da sauran kayayyaki.
Read Also:
Tawagar hadin gwiwa na yan sanda da sojoji da aka tura wajen domin hana matasan satar kayayyakin cibiyar sun gaza yin komai don dakatar da su. An gano bata garindauke da kayayyakin da suka sace a kawunansu yayinda wasu suka yi amfani da adaidaita sahu wajen kwasar nasu kayayyakin na sata zuwa kauyukan da ke makwabtaka da garin Jalingo. Wani idon shaida ya bayyana cewa cibiyar ya zama wayam babu komai kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Kayayyakin da suka sace sun hada da shinkafa, semovita, taliya, siga, gishiri da taki. Rumbun ajiyar wanda ke kusa da ofishin WAEC, an tattaro cewa yana dauke da kayayyaki mallakar hukumar birnin tarayya. A ranar Lahadi na wasu matasa sun fasa wani rumbun ajiya a yankin Jabi kuda da kotun kula da da’ar ma’aikata. Ba tare da duba kasancewar sojoji da yan sanda a wajen ba, matasan sun yashe kayayyaki daban-daban da aka ajiye a rumbun.