Fuskantar Barazana: Mawallafin Jaridar Daily Najeriya, Jafar Jafar ya Bar Gidansa 

Mawallafin jaridar Daily Najeriyan Jaafar Jaafar na fuskantar barazanar da ta tilasta shi barin gidansa tare da ɓuya a wani guri na daban.

A dan tsakankanin dai Jaafar Jaafar na fuskantar barazanar rashin tsaro daga wasu mutane da su ke yiwa rayuwarsa barazana kamar yadda jaridar PR Nigeria ta rawaito.

Wani na kusa da majiyar PR Nigeria ya bayyana cewa rayuwar Jaafar ɗin na cikin hatsari sakamakon wadansu mutane da ke bibiyar sa da ake kyautata zaton suna Da wani shiri na cutar da rayuwarsa.

Majiyar da ta buƙaci a sakaye sunanta ta ƙara da cewa mutanen na bibiyarsa a gidansa da ke Kano da kuma masaukinsa na Abuja, wanda ala tilas ya sanya ɗan jaridar ya sauya wajen zama domin tsira da rayuwarsa da kuma lafiyarsa.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here