Ban Taba Fuskantar Matsala Wajen Ciyar da Iyalina ko Biyan Kudin Makarantar Yarana ba – Magidanci Mai Yara 18
Magidanci wanda ke da mata uku a yanzu da yara 18 ya yiwa duniya albishir da cewa nan da watanni biyu sai rufe kofa da ta hudu.
Mohammed Suleiman wanda malami ne a kwalejin ilimi na Umar Bn Khattab, ya ce ko kadan baya wasa da daukar dawainiyar iyalinsa kuma bai taba gazawa ba.
Ya dai yi fice ne a shafukan soshiyal midiya a lokacin bikin babban Sallah, bayan bayyanar hotunansa tare da iyalinsa.
Magidancin nan mai mata uku da yara 18 wadanda hotunansu suka yi fice a shafukan soshiyal midiya a lokacin bikin babban Sallah, Mohammed Suleiman ya magantu a kan iyalin nasa.
Mallam Sulaiman wanda ya kasance lakcara a kwalejin ilimi na Umar Bn Khattab da ke Kaduna ya bayyana cewa ko kadan baya wasa da jin dadin iyalinsa duk da yawan da suke da shi.
Kamar yadda jaridar Punch ta wallafa hirar da aka yi da malamin, an tambaye shi game da yadda ya ji bayan fice da hotunansu suka yi a shafukan soshiyal midiya, inda ya amsa da:
“A zahirin gaskiya, al’adace da muka saba a cikin iyalina kowa zai hadu don daukar hotuna, kuma na shafe tsawon shekaru ina wallafa su a shafina. Idan kana bibiyar shafina, za ka gansu, amma a wannan shekarar sai abun ya sauya zani. Kawai sai na ga yana yawo kuma ya yi fice.”
Malamin ya bayyana cewa a lokacin da yake tasowa bai taba tunanin tara iyali haka ba domin a cewarsa idan da akwai hali toh da ya nemi idan za a basa mata a raba masa ita gida biyu saboda labarin da yake ji kan wahalar da ke cikin kula da mata da yara.
Read Also:
Ya ce da son samu ne da mata rabi zai so mallaka ba ma guda daya ba. Amma a cewarsa wannan duk tunaninsa ne a lokacin da yake matashi. Ya ci gaba da cewa da ya girma ya fahimci menene rayuwa, sai ya gane cewa kawai abun da mutum yake bukata shine jajircewa da kokari wajen neman na kai don daukar dawainiyarsu.
Ya ce:
“Na kuma ga damammaki da daman a aikata hakan ba tare da aikin ofis ba. Kuma ina kallonsa a matsayin hanyar daukar dawainiyar mata saboda akwai su da yawa wadanda suke ba tare da mijin aure ba. Yanzu ina da mata uku, kuma ina fatan sake auren daya nan da watanni biyu.”
Da aka tambaye shi kan ko yana manta sunayen yaran nasa, sai yace a matsayinsa na Musulmi dukka yaransa na dauke da sunaye ne daga cikin tsarkakken sunayen Allah, don haka ya jero su ne bi da bi. Ya kuma ce suna da sunaye da ake masu inkiya da su kuma duk ya sansu.
Malamin ya kuma bayyana cewa yaransa 18 ba 19 ba kamar yadda ake ta yayatawa domin yana rike da yaran yan uwansa, inda yace yana rikon yara bakwai baya ga wadanda ya haifa.
Da yake magana kan yadda yake tafiyar da kishi a tsakanin matansa sai ya ce shi mutum ne mai adalci a tsakaninsu don haka ne ma suka amince har suka yi tarayya wajen daukar hoto tare.
Ya jaddada cewa shi tsayayye ne a kan gidansa amma duk da haka suna dan samun sabani da ba a rasa ba. Kan yadda yake daukar dawainiyar iyalinsa ta bangaren jin dadi ya ce:
“Magana ta gaskiya, watakila saboda ina da hazaka ne ta bangaren nema, aiki da tafiye-tafiye. Zan iya aiki a ko’ina. Na tuna na taba aiki da kamfanin dakon kaya na jiragen sama, tashi daga Saudiyya zuwa Najeriya da sauran wurare. Ban taba fuskantar matsala wajen ciyar da iyalina ko biyan kudin makarantar yarana ba.
“Harma, an karramani a makarantar yarana a matsayin daya daga cikin iyaye da ke biyan kudin makaranta kan lokaci. Diyata na jami’a, dana na a kwalejin kimiyya, kuma babu lokacin da na taba shiga mawuyacin hali saboda ina tsara abubuwa.”