Ana Fuskantar wani ya na yi a Najeriya – Sa’ad Abubakar
Sultan na Sakkwato, Alhaji Abubakar Sa’ad III, ya koka a kan mawuyacin halin da kasar ke ciki a yanzu.
Sarkin Musulmin ya bayyana cewa tsadar albasa kadai da ake fama dashi a kasar nan ya isa nuni ga cewar tattalin arzikin kasar na cikin wani yanayi.
Ya kuma yi tsokaci a kan matsalar rashin tsaro da ke kara tabarbarewa a kulla-yaumin.
Read Also:
Mai martaba sarkin Musulmi kuma Sultan na Sakkwato, Alhaji Abubakar Sa’ad III, ya yi tsokaci a kan matsalolin tsaro da matsin tattalin arziki da Najeriya ke fama da su a yanzu haka.
Sultan, da yake jawabi a wajen taron majalisar shugabannin addinai ta kasa, ya bayyana cewa yadda albasa ta yi tsada ya tabbatar da girman wahalar tattalin arzikin da ake ciki a yanzu a Najeriya
Hakan na kunshe ne a cikin wata wallafa Majalisar ƙoli ta harakokin addinin musulunci tayi a shafinta na Twitter.
“Yadda albasa ta yi tsada a Najeriya a yau alamu ne da ke nuna mawuyacin halin da tattalin arzikin kasar ke ciki a yanzu. Ba wai mun rasa shawarwari da maganin matsalolinmu bane. Abunda muka rasa shine tunanin manufofi.”