Wasu Fussatatun Matasa Sun Harbe Wani Dan Sanda Har  Cikin Caji Ofis

Wata zanga-zanga ta barke ranar Juma’a a babban ofishin rundunar ‘yan sanda da ke yankin Ado a jihar Ekiti.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ya ce masu zanga-zangar suna zargin cewa ‘yan sanda suna kokarin cutar dangin wani mamaci.

Rundunar ‘yan sanda ta zargi masu zanga-zangar da mayar da martani a yayin da aka yi harbi sama domin tarwatsasu daga ofishin.

An harbe wani jami’in rundunar ‘yan sandan Najeriya yayin da wasu fusatattun matasa suka shirya zanga-zanga a jihar Ekiti, ranar Juma’a.

Lamarin ya faru ne yayin da fusatattun matasan suka mamaye babban ofishin rundunar ‘yan sanda da ke Ado a wata zanga-zangar nuna bacin ransu a kan kisan wani dan achaba da wani direban mota ya yi.

TheCable ta ce majiyarta ta sanar da ita cewa matasan sun fusata tare da mamaye ofishin bayan rundunar ‘yan sanda ta rike gawar dan achabar da kuma kudin diyya N470,000 da direban ya biya dangin mamacin.

“Dangin mamacin sun mamaye ofishin ‘yan sanda domin nuna fushinsu a kan rike gawar dan uwansu da kuma kudin diyyar ransa da aka bayar, sun mamaye ofishin ne domin tilasta ‘yan sanda sakin gawar da kudin,” a cewar majiyar.

Sannan ya cigaba da cewa; “bayan ‘yan sandan ofishin sun fuskanci cewa al’amura sun fara rincabewa, sai suka fara sakin barkonon tsohuwa da kuma harbi sa domin tarwatsa masu zanga-zangar.

“A irin harsashin da suke harbawa sama ne, sai ya dawo ya samu kafar dan sanda, wanda daga bisani ya mutu saboda asarar jini mai yawa da ya yi.”

Sai dai, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ekiti, Sunday Abutu, ya ce kuskure ne tare da yin gaggawar fadin cewa harsashin ‘yan sanda ne ya hallaka jami’in.

Kazalika, ya tabbatar da mutuwar dan sandan tare da bayyana cewa matasa sun fara zanga-zanga ne bayan samun labarin jita-jitar cewa an biya N150,000 a matsayin diyyar dan achaban da aka kashe.

Ya kara da cewa masu zanga-zangar sun fusata ne bisa zargin cewa jami’an ‘yan sanda zasu cuci dangin mamacin.

“Da gaske ne cewa jami’an ‘yan sanda sun bar direban da dangin dan achabar domin su daidaita kansu, wanda daga bisani suka amince direban zai biya N440,000, wacce kuma ya biya dangin mamacin kai tsaye,” a cewarsa.

Kakakin ya kara da cewa, “an yi yarjejeniyar cewa, daga cikin kudin, za’a bawa wanda ya siyawa marigayin N150,000, a matsayin kudin babur dinsa, wanda hakan shine silar barkewae zanga-zangar.

“Jami’anmu sun yi kokarin tarwatsa masu zanga-zangar bayan sun fara fito da makamai kala-kala tare da bukatar a sakar musu direban da ake tsare da shi.

“Sai dai, jami’anmu sun sha mamaki, matasan sun bijire, kuma da aka yi harbi sama domin basu tsoro, sai suka mayar da martani ta hanyar fara harbin jami’anmu ta kowanne bangare, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar jami’i guda.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here