Fyaɗe ya ƙaru Kashi 218% a Sudan ta Kudu – UNMISS
Tarzomar jinsi da fyade masu alaƙa da rigingimu na ƙaruwa a Sudan ta Kudu, yayin da faɗa ke raguwa a ƙasar, bisa rahoton ofishin Majalisar Dinkin Duniya a kasar (Unmiss).
A cikin rahoton, ofishin ya ce akwai ƙaruwar kashi 218% a fyaɗe da fyaɗen taron dangi tsakanin watan Afrilu da Yuni.
Read Also:
“Wannan tashin goron zabo na fyade da tarzomar jinsi ba za a amince da shi ba, kuma ya fi shafar mata da yara mata sosai,” a cewar Nicholas Haysom, shugaban Unmiss.
Fadace-fadace tsakanin kananan al-ummomi na ci gaba da shafar fararen hula, biyo bayan arangama da aka sha yi tsakanin mayaƙan sa kai da dakarun gwamnati.
Fitowar rahoton ya zo a lokaci daya da isar ƙwararru uku daga hukumar ‘yancin kai ta Majalisar Dinkin Duniya a Sudan ta Kudu.
Za su hadu da jami’an gwamnati da wakilan kungiyoyin farafen hula da jami’an diflomasiyya dangane da sakamakon rahoton.