Fyaɗe ya Yawaita a Yaƙin Sudan – MDD
Wani binciken Majalisar Ɗinkin Duniya ya gano cewa fyaɗe ya yawaita a yaƙin da ake yi a Sudan inda ake zargin dakarun ƙungiyar RSF da aikatawa.
Read Also:
Binciken ya gano cewa dakarun RSF na garkuwa da mata da yara aƙalla waɗanda shekarunsu suka fara daga takwas inda suke mayar da su ƙwarƙwara.
An gano yadda ake yi wa maza da mata fyaɗe sosai a cikin binciken.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce dukkan ɓangarorin biyu na sojojin Sudan da dakarun RSF na amfani da cin zarafin ta hanyar lalata wajen tsoratar da fararen hular da suke zargi na da alaka da maƙiyansu.
Daga bisani binciken ya buƙaci a tura dakaru na musamman Sudan ɗin domi kare