Gobara ta Kama Hedikwatar Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Najeriya ta NPA

 

Rahotanni sun ce Hedikwatar Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Najeriya ta NPA ta kama wuta.

An rawaito cewa, dukiya mai darajar miliyoyin nairori sun lalace yayin da gobarar ta kame wasu ofishoshi.

An samu nasarar kashe gobarar, inda aka mika godiya ga hukumomin da suka kawo dauki a lamarin.

Legas – Kadarori masu darajar miliyoyin nairori sun lalace sakamakon gobarar da ta tashi a Hedikwatar Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Najeriya (NPA), da ke kan titin Broad da ke birnin Legas.

An ce gobarar ta tashi ne sanadiyar dagulewar wutar lantarki a yau Laraba 22 ga watan Satumba, in ji rahoton Daily Sun.

Gobarar ta shafi ofisoshi uku a hawa na 6 na ginin amma ba a samu rahoton rasa rai ba.

Wasu ma’aikata, wadanda suka nemi a sakaya sunan su, sun ce suna shirin fara aikin ranar ne lokacin da gobarar ta kama.

Ma’aikatan sun ce an nemi wadanda ke kan benen da abin ya shafa su kasance a wani wuri a kasa inda jami’an tsaro suka lissafa adadin wadanda ke bakin aiki.

Babban Manaja a fannin Sadarwa da Dabarun Sadarwa na NPA, Olaseni Alakija, wanda ya tabbatar da afkuwar lamarin, ya ce jami’an hukumar kashe gobara ta NPA sun gaggauta zuwa wurin da abin ya faru, kuma nan take suka shawo kan gobarar.

Alakija ya ce bisa ka’idojin kariya, tun daga lokacin aka killace ginin da abin ya shafa kuma ana ci gaba da bincike don gano ainihin musabbabin gobarar, Daily Trust ta rawaito.

Abubuwan da suka lalace

Da yake bayyana irin asarar da aka tafka, Alakija ya ce an samu asarar wasu abubuwan ciki ofis, inda yake cewa:

“Gobarar ta shafi ofishi daya inda aka rasa na’urorin kan teburi guda 2, wasu tebura, kujeru da sauran kayan ofis. Wasu ofisoshin biyu da ke kusa da su hayaki da toka sun shafe su.

Ya kuma mika godiya ga jami’an kashe gobara da suka kawo taimakon gaggawa a kan lokaci, jami’an tsaro da suka shiga lamarin har ma dukkan masu ruwa da tsaki a wajen.

Ku tuna cewa dukiya mai darajar da ta kai biliyoyin nairori ta lalace lokacin da tsagerun ‘yan daba suka cinnawa hedkwatar NPA wuta yayin zanga-zangar @EndSARS.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here