Wajibi ne Mutum ya Gabatar da NIN Kafin Ayi Masa Rijista – Ministan Sadarwa
Bayan watanni da sanya takunkumi kan rijistan layukan waya, ministan sadarwa ya dage.
Pantami ya ce daga yanzu wajibi ne mutum ya gabatar da NIN kafin ayi masa rijista.
A cewarsa, Buhari ya jinjinawa ma’aikatar bisa namijin kokarin da sukayi Gwamnatin tarayya ta bada izinin cigaba da rijistan sabbin layukan waya bayan wata da watanni da sanya takunkunmin yin haka.
Ministan Sadarwa, Dakta Isa Ibrahim Ali Pantami, ya bayyana hakan ne ta bakin hadiminsa, Dr Femi Adeluyi, ranar Alhamis a shafin Tuwita. Ministan ya ce za’a cigaba da rijistan amma da sharadin sai mutum na da lamban katin zama dan kasa, NIN.
Read Also:
Pantami ya ce an yanke shawaran cigaba da rijistan sabbin layuka ne bayan amincewar shugaba Buhari da sabon tsarin rijistan layuka da ma’aikatarsa ta samar.
“An kammala gyara-gyare kan tsarin bisa ga umurnin shugaban kasa inda aka wajabta amfanin da lambar NIN don rijistan sabon layi a jiya, 14 ga Afrilu, 2021,” jawabin yace.
“Dr Pantami ya gabatar da tsarin ga shugaba Muhammadu Buhari…
kuma (Buhari) ya jinjinawa ministan bisa kokarinsa wajen kawo cigaba sashen tattalin arzikin zamani da kuma atisayen hada layukan waya da NIN.”
“Za’a fara aiwatar da sabon tsarin ranar Litnin, 19 ga Afrilu 2021. Hakazalika za’a cigaba da bada sabbin layuka da kuma sauran abubuwan da aka dakatar a ranar.
“Bugu da kari, Ministan ya umurci NCC da NIMC su tabbatar da cewa masu rijistan layukan da jama’a sun bi tsarin sau da kafa.”