Hukumar EFCC ta Sako Tsohon Gwamnan Jahar Imo, Rochas Okorocha

 

Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta sako tsohon gwamnan jahar Imo, Rochas Okorocha.

Hadiminsa tsohon gwamnan ya tabbatar da cewa Okorocha ya koma gidansa da ke Maitama a Abuja.

EFCC ta kama Okorocha ne a ranar Talata a ofishinsa ta kuma tafi ta tsare shi na kwanaki biyu kan zargin almundahana lokacin yana gwamna Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati, EFCC, ta sako tsohon gwamnan jahar Imo, Rochas Okorocha bayan ya yi kwanaki biyu a hannunta yana amsa tambayoyi.

Hadimin Okorocha, wanda ya yi magana da Daily Trust a wayar tarho ya ce an sako tsohon gwamnan misalin karfe 5.45 na yamma kuma a halin yanzu yana gidansa da ke Maitama a Abuja.

Da aka tuntube shi, mai magana da yawun hukumar na yaki da rashawa, Wilson Uwujaren ya ce a bashi lokaci kafin ya yi tsokaci kan lamarin.

A ranar Talata ne jami’an EFCC suka kama dan majalisar a ofishinsa da ke Unity House Garki Abuja misalin karfe 4 na yamma.

Ana zargin Okorocha, wanda ya yi mulki matsayin gwamna a jahar Imo daga shekarar 2011 zuwa 2019 da laifin almundaha da almubazaranci da kudi amma ya musanta hakan.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here