Shugaban Sojojin Gabon, Brice Nguema na Shirin Tattaunawa Kan Miƙa Mulkin ƙasar
Shugaban sojojin Gabon, Brice Oligui Nguema, ya kaddamar da shirin tattaunawa da nufin magance lokacin mika mulki da kuma tsara makomar kasar, kamar yadda wani shafin intanet na labarai na aLibreville mai zaman kansa ya ruwaito, a ranar 11 ga Maris.
Nguema ya hau ƙaragar mulki bayan hamɓarar da shugaba Ali Bongo a watan Agustan 2023.
Taron wanda aka tsara zai gudana ne a babban birnin ƙasar Libreville daga ranar 2 zuwa 30 ga watan Afrilu, tattaunawar za ta kunshi halartar jam’iyyun siyasa daban-daban.
Read Also:
Archbishop Jean Patrick Iba-Ba shine Jagoran tattaunawar.
Tattaunawar na da nufin tantance tsawon lokacin mika mulki da kuma gabatar da sauye-sauye na siyasa da na tattalin arziki da na zamantakewa ga al’ummar ƙasar bayan samun nasarar juyin mulkin, kamar yadda bayanai suka nuna daga wata sanarwa da shugaban sojojin ya fitar.
Bugu da kari, gwamnatin da sojoji ke jagoranta ta fitar da shirin aiwatar da sabon kundin tsarin mulki ta hanyar zaben raba gardama zuwa karshen shekarar 2024.
Nguema ya kasance yana tuntubar jami’an siyasa na cikin gida da cibiyoyin yanki, amma ya kau da kai daga ɗaukar kwararan alkawura kan ci gaba da mulki.