Muna Kira ga Hukumomin Tsaro da su Gaggauta Kama Wadanda Suke da Hannu a Kashe Matafiya Musulmai – CAN
Kungiyar kiristoci ta CAN ta bayyana matsayarta game da kashe musulmai da aka yi a garin.
Jos Wannan ya biyo bayan sanya dokar hana fita da gwamnatin jahar ta yi da yammacin ranar Asabar.
CAN ta ce, dole ne jami’an tsari su kamo dukkan masu hannu a wannan mummunan kisa da ya faru..
Jos, Filato – Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN), reshen jahar Filato, a ranar Lahadin da ta gabata ta yi Allah wadai da kisan wasu matafiya musulmai 25 a hanyar Rukuba, a karamar hukumar Jos ta Arewa a jahar.
Rev. Fr. Polycarp Lubo, shugaban CAN a jahar, ya bukaci hukumomin tsaro da su gaggauta zakulo wadanda suka aikata danyen aikin, Daily Nigerian ta ruwaito.
Read Also:
Legit Hausa ta rahoto cewa wasu matasa da ake zargin ‘yan Irigwe ne sun kai hari kan motocin bas guda biyar dauke da matafiya Musulmai sama da 90, sun kashe mutane 25 tare da jikkata wasu da dama.
Mista Lubo ya kuma yi Allah wadai da kashe-kashen da ke faruwa a kananan hukumomin Bassa, Riyom, Jos ta Kudu da Barkin Ladi.
A cewarsa:
“Shugabancin CAN gaba daya ya la’anci wadannan hare-hare tare da rokon jami’an tsaro da su tabbatar da an dawo da zaman lafiya.
CAN ta tura sakon jaje ga iyalan wadanda aka cutar ”Muna jajantawa ga iyalan wadanda suka rasa ‘yan uwansu, da kuma wadanda aka raba da muhallansu ko kuma aka yi musu lahani ko wace iri.
“Muna kira ga hukumomin tsaro da su gaggauta cafke duk wadanda ke da hannu, don kawo karshen kashe-kashen da basu dace ba.”
Mista Lubo ya ce kungiyar za ta ci gaba da aiki don tabbatar da zaman lafiya a jahar.