Mutane 21 Sun Rigamu Gidan Gaskiya Sanadiyyar Rugujewar Gada a Jahar Jigawa

 

Akalla mutane 21, ciki har da mutane 11 masu neman aikin soja, an ba da rahoton mutuwarsu a ranar Lahadi yayin da wata gada ta ruguje a Karamar Hukumar Gwaram ta Jahar Jigawa.

Mazauna garin sun ce gadar ta rushe ne sakamakon ambaliyar ruwa.

Shugaban kungiyar fararen hula ta jahar Jigawa, Musbahu Basirka, ya shaida wa Premium Times cewa wadanda abin ya rutsa da su na cikin motar bas ne daga Kano zuwa Adamawa lokacin da lamarin ya faru.

Mista Basirka ya ce wadanda suka mutu sun hada da wata matashiya amma an bayar da rahoton cewa daya daga cikin masu neman aikin sojan ya tsira da karayar kafa.

Karin bayani na nan tafe…

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here