Ganduje ne Yafi Cancanta ya Zama Abokin Tafiyar Tinubu – Hadimin Ganduje
Ana tsaka da neman ganin an zabi wanda zai zama abokin tafiyar Bola Tinubu a matsayin mai rike da tutar jam’iyyar APC a zaben 2023, hadimin gwamnan jihar Kano ya ce ubangidansa ne yafi cancanta.
Ya fadi hakan ne yayin zantawa da manema labarai a karshen mako a Kano, inda ya ce a halin yanzu Ganduje ne kawai zabin da jam’iyyar ke dashi, duba da irin nagarta da halin dattakunsa da ya nuna.
Ya kara da cewa, Ganduje ne kadai wanda ya fito karara ya marawa Asiwaju baya duk da yadda wasu masu rike da mukaman arewa suka ji tsoron yin hakan, sannan bai da kabilanci tunda har ya dauki ‘diyarsa ya ba bayarbe aure.
Kano – Ana tsaka da neman ganin waye dai zama mataimakin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, mai rike da tutar takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, mai bada shawara ta musamman ga Abdullahi Umar Ganduje a kafafan sada zumunci, Shehu Isa ya bayyana dalilan da yasa ya ke ganin ya kamata jam’iyyar da Tinubu su dauki Ganduje a matsayin abokin tafiyarsa a zaben 2023.
Read Also:
Isa wanda ke kokarin ganin ya gamsar da cewa bai saba doka ba tikitin Musulmi da Musulmi, inda ya ce Ganduje ne yafi cancantar rike tutar takarar shugaban kasa a jam’iyyar baya ga Tinubu.
Vanguard ta rawaito cewa, hadimin ya fadi hakan ne yayin zantawa da manema labarai a Kano karshe sati.
A cewarsa Isa, “Idan za a yi dubi da irin mahimmanci, kafa tarihi a lokacin aiki, siyasa da irin dattakun da ya ke da shi, Ganduje ne kadai zabin da APC ke da shi.
“Ganduje ne a gaba daya arewa wanda ya fito karara ya tsayawa kamfen din Tinubu duk da irin kalubalen kin amincewa da shi da mutane da dama za su iya, yayin da masu rike da mukamai na arewa suka ji tsoron fitowa fili su mara masa baya.
“Bai da kabilanci, duk da kasancewarsa Fulani, ya bai wa bayarbe auren ‘diyarsa. Ko Tinubu zai fi samun natsuwa yin aiki tare da shi a matsayin abokin tafiyarsa.
“Idan aka dauki Ganduje a matsayin mataimakin shugaban kasa, tabbas zai yi kokarin kawo karshe matsalolin makiyaya, masu garkuwa da mutane, ta’addanci da sa sauran munanan ayyukan da ke addabar kasar nan kasancewarsa kakakin bafulatani,” a cewarsa.
“Game da kalubalen tikitin Musulmi da Musulmi, Isa ya ce, hakan baya cikin kundin tsarin mulki, amma Kaduna ta fara gwada wa kuma tun daga lokacin nan, jihar na zaune cikin kwanciyar hankali, ba tare da rikicin kabilar da aka san jihar da shi ba,”