Ganduje ya Magantu Kan Batun Tsige Sanusi II
Jihar Kano – Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya yi martani kan raɗe-raɗin da ke cewa yana da hannu a shirin tsige Muhammadu Sanusi II daga kan sarautar Kano.
Ganduje ya ƙaryata raɗe-raɗin inda ya bayyana su a matsayin tsantsagwaron ƙarya.
Ganduje ya musanta zargin da ake yi masa
Jaridar Leadership ta ce Ganduje ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da babban mai taimaka masa na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Cif Oliver Okpala, ya fitar.
Read Also:
Shugaban na APC yana mayar da martani ne kan wani rahoto da ke yawo a kafafen sada zumunta wanda ya yi iƙirarin cewa Ganduje yana jagorantar tsige Muhammadu Sanusi II daga kan sarautar Kano.
Me Ganduje ya ce kan tsige Sanusi II
Da yake mayar da martani, Ganduje ya ce babu ƙamshin gaskiya a cikin iƙirarin, inda ya nanata cewa ba shi da hannu a zargin da ake yi na shirin tsige Sanusi II.
“Yana da kyau a sani cewa Ganduje ba shi da wata alaƙa ta naɗawa ko tsige Sarki Muhammadu Sanusi II a Kano.”
“Ya kamata a sani cewa Ganduje yanzu ba shi ba ne gwamnan Kano ko shugaban majalisar dokokin jihar Kano, saboda haka ba shi da wata alaƙa da sarautar Kano.”
– Cif Oliver Okpala
A cewar sanarwar, Ganduje ya ce ba shi da hannu a wajen ba da ga shawara ga Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya haƙura da sarautar Kano.