Majalisar Malaman Jihar Oyo ta ba wa Gwamna Ganduje Mukamin Alaadini na Kasar Yarbawa

Gwamna Abdullahi Ganduje ya samu sabuwar sarautar mai riko da addinin na kasar Yarbawa karshen makon da ya gabata.

Wannan ya biyo bayan nadin sarautar da Olubadan of Ibadan ya masa na Aare Fiwajoye na kasar Ibadan.

Gwamna Ganduje suruki ne ga tsohon gwamnan jihar Oyo, Marigayi Abiola Ajimobi.

Ibadan – Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya amu mukamin Alaadini na kasar Yarbawa daga wajen Majalisar Malaman kasar Oyo, Kudu maso yammacin Najeriya.

Kasar Oyo ce cibiyar daular mulki na yankin Yarabawa.

Mukamin Alaadini na nufin mai riko da addini.

Hadimin Gwamna Ganduje na hotuna, Aminu Dahiru, ya fitar da jawabi da hotunan kan wannan nadi da akayiwa Ganduje, a cewarsa:

“A ranar Asabar 18 ga watan Yuni ne Majalisar malamai ta yankin jihohin yarabawa wanda suke da cibiya a Ibadan Babban birnin jihar Oyo suka baiwa Mai Girma Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR, Sarautar ALAUDDEN OF YORUBAWA (ALADDIN OF YORUBA) Karkashin Jagorancin Shugaban majalisar limamai da malamai na Jihar Oyo, Sheikh Abdulganiyy Abubakar (AGBOLOMOKEKERE).”

Shugaban majalisar malaman, Sheikh Abdulganiyy Abubakar, ya bayyana cewa:

“Ana bada sarautar ne kadai ga Musulmi mai riko da addini da kuma yiwa addinin hidima inda binciken su ta tabbatar musu da cawa Mai Girma Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje shine ya cika wannan sharudan ya kuma taya shi murna bisa hakan.”

Kalli hotunan:

Ganduje Alaadini 1

Ganduje Alaadini 2

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here