Jami’an Tsaro Sun Ceto Mutane 14 Daga Hannun ‘Yan Bindiga a Jihar Zamfara

Jami’an tsaro a jihar Zamfara a Najeriya sun ceto mutum 14 daga hannun yan bindiga a garuruwan Nasarawar Wanke da Rijiya da ke karamar hukumar mulkin Gusau.

A sanarwar da jami’in hulda da jama’a na Rundunar Yan sanda a jihar SP Mohammed Shehu ya fitar, ya ce an kubutar da mutanen ne a dajin Kuncin Kalgo, kuma sun hada da mata 10, da maza biyu, da jarirai biyu.

SP Muhammad Shehu ya ce sun samu bayanan sirri kan inda aka boye mutanen, kuma aikin ceton na hadaka ne da wasu yan kishin jiha da ke son ganin an samu zaman lafiya a Zamfara.

Tuni an mika mutanen ga yan uwansu, bayan jawabin manema labarai a hedikwatar rundunar yan sandan da ke Gusau.

Jihar Zamfara na daga cikin jihohin Arewacin maso Yammacin Najeriya da ke fama da hare-haren yan bindiga da ke garkuwa da mutane don neman kudin fansa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here