Gwamna Ganduje ya Shawarci ‘Yan Najeriya da Su Koma ga ALLAH

 

Gwamna Ganduje na jahar Kano ya shawarci ‘yan Najeriya da su koma ga Allah.

Ganduje ya yi wannan kira ne a wani taron tunawa da ranar haihuwar Bola Tinubu.

Ya kuma kirayi ‘yan Najeriya da su hada kai don kawo ci gaba da habaka darajar Najeriya.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jahar Kano a ranar Litinin ya ce dangane da batun hadewar kasa, dole ne duk ‘yan Najeriya su koma ga Allah.

Ganduje ya bayyana haka ne a jawabinsa na maraba a taro na 12 na zagayowar ranar haihuwar Bola Tinubu da ya gudana a jihar Kano.

Taron tattaunawar, wanda aka shirya don bikin cika shekara 69 na Tinubu, shugaban jam’iyyar APC na kasa, an masa taken:

“Hadin kan mu, arzikin mu: Wajibi ne ga hadin kan kasa don girma da ci gaba”.

Ganduje ya yarda cewa matakin hadin kan Najeriya a halin yanzu yana cikin wani mawuyacin hali, yana mai cewa idan ba a yi wani abu ba don sauya kanun labarin, to lallai kasar na kusa da durkushewa kasa.

“Dangane da batun hadewar kasa, duk ‘yan Najeriya dole ne su koma ga Allah,” in ji shi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here