Ba da Gangan Aka ƙi Kula da Tawagar Super Eagles ba, Duk da mu ma an yi Mana Hakan a Najeriya – LFF

 

Hukumar ƙwallon ƙafa ta Libya (LFF) ta ce ba da gangan aka bar tawagar Super Eagles ta Najeriya yashe a filin jirgi ba, duk da cewa su ma an yi musu hakan a Najeriyar.

“Mun damu matuƙa kan abin da ya faru da tawagar ƙwallon ƙafan Najeriya, gabanin wasan neman gurbin shiga gasar Kofin Afirka,” in ji sanarwar da ta wallafa a shafinta na X.

“Dduk da dai mun yi nadamar abin da ya faru, muna kuma jan hankali cewa irin wannan matsala tana iya faruwa bisa kuskure a kowanne lokaci, ko dai saboda ƴan gyare-yare a filin jirgi ko saboda binciken jami’an tsaro ko kuma wasu ƙalubale na daban daga jiragen saman ƙasa da ƙasa.

”Muna matuƙar mutunta Najeriya, kuma muna bayar da tabbacin cewa ba da gangan aka samu wannan matsala ta karkatar da jirgin tawagar Super Eagles ba.

“Mu ma mun fuskanci irin wannan matsala lokacin da muka je Najeriya a makon da ya gabata, amma ba mu zargi hukumomi da aikata hakan da gangan ba.”

Bayan wasan farko da Najeriya ta doke Libya 1-0 a birnin Uyo na jihar Akwa Ibom a ranar Juma’a, an tsara buga wasa na biyu a birnin Benghazi na Libya ranar Talata.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here