Mutane 26,000 ne Suka Sami Damar Ganin Gawar Sarauniya Elizabeth a Edinburgh
Read Also:
A birnin Edinburgh kuwa, gwamnatin kasar Scotland ta wallafa wani sakon Tiwita da ke cewa layukan mutanen da ke son ganin gawar Sarauniya a cocin St Giles sun kare.
Gwamantin ta ce fiye da mutum 26,000 ne suka sami damar karrama Sarauniyar – ciki har da wadanda suka kwana suka jiran a ba su damar shiga cocin.
Wasunsu sun ce an shaida mu su cewa za su rasa damar kafin a dauke ta daga cocin zuwa birnin Landan.