Tukunyar Gas ta yi Sanadiyyar Raunata Mutane da Dama, Shaguna da Gidaje Sun ƙone a Jigawa

 

Mutane da dama sun ji raunuka, shaguna da gidaje sun ƙone yayin da wata Tukunyar Gas ta fashe a jihar Jigawa.

Kakakin hukumar NSCDC reshen jihar, Adamu Shehu, yace lamarin ya faru jiya Litinin da daddare a ƙaramar hukumar Babura.

Har yanzun babu wanda ya rasa rayuwarsa sakamakon fashewar yayin da wasu ke kwance a Asibiti, inji kakakin NSCDC.

Jigawa – An tattaro cewa mutane da dama sun ji raunuka daban-daban yayin da Gidajen mutane da Shaguna suka ƙone biyo bayan fashewar wata Tukunyar Gas a ƙaramar hukumar Babura, jihar Jigawa.

Kakakin rundunar tsaron Sibil Defence (NSCDC) reshen jihar Jigawa, Adamu Shehu, ya tabbatar da aukuwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar da safiyar Talata.

Yace lamarin ya faru ne lokacin da wata babbar Motar dakon kaya maƙare da Tukunyar Gas ta yi bindiga a Babura, kamar yadda Jaridar Punch ta rahoto.

Kakakin NSCDC yace Gidaje da yawa da shagunan al’umma sun ƙone sakamakon faruwar lamarin, inda ya ƙara da cewa mutane da dama sun jikkata, amma har yanzu ba bu wanda ya mutu.

“Mummunan lamarin ya auku ne jiya da daddare, ranar Litinin 12 ga watan Satumba, 2022 da misalin ƙarfe 9:00 na dare,” Inji shi.

Wane mataki mahukunta suka ɗauka?

Adamu Shehu ya bayyana cewa tuni aka garzawa da mutanen da suka jikkata babban Asibitin Babura domin ba su kulawar lafiya ta musamman.

A jawabinsa yace, “An tura jami’an kwana-kwana daga ƙaramar hukumar Haɗejia zuwa yankin domin su shawo kan wutar da ta tashi.”

Bugu da ƙari, mai magana da yuwun NSCDC a Jigawa yace har yanzun babu cikakken bayani kan makasudin abinda ya jawo fashewar, a cewarsa duk abinda bincike ya gano za’a sanarwa al’umma.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here