JTF: An Gano Gawar Jami’i Hadin Gwiwa a Karkashin Gadar Gwagwalada a Abuja

Wasu mazauna sun gano wata gawa ta wani jami’in JTF a karkashin gadar Gwagwalada a Abuja.

Rahoton ya bayyana cewa, da alamu an sace jami’in ne kafin daga bisani aka kashe shi aka jefar da gawarsa.

A halin yanzu an ruwaito cewa, rundunar ‘yan sanda sun dauke gawar, suna kan bincike kan lamarin.

Abuja – An gano gawar wani jami’in hadin gwiwa (JTF) a gadar Gwagwalada da ke kan hanyar Abuja zuwa Lokoja a babban birnin kasar.

Daily Trust ta gano cewa gawar jami’in, wanda ke sanye da kaki, ya huje da harbin harsashi.

Matafiya sun gano gawar, wacce daga baya jami’an tsaro suka dauke ta, ranar Talata 3 ga watan Agusta, 2021.

Wani shaida, wanda aka bayyana sunansa da Gabriel, ya ce an gano gawar ne a gaban Otal din Brifina da ke Gwagalada.

Ya ce daga baya wasu ‘yan sandan Gwagwalada sun tafi da gawar, wadanda suka zo wurin da motar sintiri.

Wata majiyar kuma ta ce mai yiwuwa an yi garkuwa da jami’in na JTF ne sannan daga baya wadanda suka sace shi suka kashe suka kuma jefar da gawarsa a kan babbar hanya.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya ASP Maryam Yusuf, ta tabbatar da gano gawar amma ta ce mai yiwuwa jami’in ya yi hadari ne.

ASP Maryam Yusuf ta ce rundunar na bincike kan lamarin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here