Mun Gano Tushen Harin da ya yi Sanadin Rasa Shugaban Miyetti Allah – Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya

Rundunar yan sandan Najeriya a Abuja ta ce ta gano tushen harin da ya yi sanadin rasuwar shugaban Miyetti Allah.

Kwamishinan Yan Sanda na Abuja, wadanda mambobin na MACBAN suka siyawar shanu ne suka bi sahunsu suka kai musu hari tare da kwace kudin.

Rundunar yan sandan ta ce a halin yanzu ta yi nasarar gano tushen lamarin kuma bincike na tafiya amma ba za ta bayyana dukkan matakan da ta ke dauka ba.

FCT, Abuja – Gwamnatin Babban Birnin Tarayya Abuja ta ce ta yi bincike ta kuma gano wadanda suka kai wa mambobin kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah hari a Gwagwalada, Abuja, rahoton The Punch.

A kalla mambobin kungiyar hudu ne ciki har da shugaban kungiyar aka kashe a makon da ta gabata.

An rahoto cewa suna dawowa ne daga kasuwar Izom a Jihar Niger a lokacin da yan bindigan suka kai musu hari a kusa da kauyen Daku a Abuja.

An kuma sace wasu mutane hudu yayin da wasu da dama suka jikkata.

Sakatare Janar na MACBAN, Ngelzeerma Usman ya shaida wa wakilin The Punch cewa wadanda suka sace mutanen suna neman a biya fansar N100m.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here