‘Yan Bindiga Sun Kashe Sojojin Benin Biyar

 

An kashe sojojin Benin biyar a cikin wani harin da ‘yan bindiga suka kai a gandun dajin Pendjari da ke arewacin kasar.

Yankin arewacin Benin na fuskantar karuwar hare-haren masu ikirarin jihadi.

Kazalika yankin ya zama wurin daukar sabbin ‘yan tayar da kayar baya, saboda kusancin yankin da yankunan da ake fama da rikici a makwabtan kasashen Burkina Faso, da Nijar da Najeriya.

A shekarar 2019, an kashe wani dan-jagorar masu yawon bude-ido sannan aka sace ‘yan kasar Faransa biyu.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here