Gwamna Samuel Ortom ya Gargaɗi Masu Shirin Maguɗin Zaɓen 2023

 

Gwamnan jahar Benuwai, Samuel Ortom, ya gargaɗi masu shirin maguɗin zaɓe a jahar da su bar wasiyya kafin fitowa gida.

Gwamnan ya faɗi haka ne yayin zantawa da manema labarai a Makurdi jim kaɗan bayan dawowarsa daga Abuja.

APC reshen jahar Benuwai tace maganganun gwamnan na nuni da wata makarkashiya da ake shiryawa

Benue – Gwamna Samuel Ortom na jahar Benuwai, ya gargaɗi duk wasu masu shirin maguɗin zaɓe a 2023 da su fice daga jahar, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Gwamna yace idan suka ki kuma to kar su zargi kowa su zargi kansu a kan duk abinda ya faru da su lokacin zaben 2023.

Gwamnan ya yi wannan gargaɗin ne yayin zantawa da manema labarai a Makuɗi jim kaɗan bayan dawowarsa daga taron gwamnonin PDP a Abuja.

Menene matsayarku kan tura sakamako ta Na’ura?

Gwamna Ortom yace Najeriya ta kai duk matakin da ya kamata kuma bai kamata a cigaba da harkar zaɓe a rubuce ba kamata ya yi a fara amfani da fasahar zamani.

Leadership ta rahoto a jawabinsa, Ortom yace:

“Ya kamata shugaban ƙasa ya sake tunani, ina mai ba shi shawara kada ya sanya hannu a kan dokokin zaɓe da aka yiwa garambawul ba tare da an sanya tura sakamako ta na’ura ba.”

“Mu anan jahar Benuwai mun kammala shiri, duk wanda ya zo zai mana maguɗin zaɓe a 2023, to ya bar wasiyya tun kan ya fito gida.

“Babu wanda zai zo ya canza mana sakamakon zaɓe ba cin mu ne mafiya rinjaye, ba zai taɓa yuwuwa ba.”

Wai meyasa PDP batasan komai ba sai maguɗin zaɓe?

Da yake martani ga gwamnan, Kakakin jam’iyyar APC reshen jahar, James Ornguga, yace Ortom da jam’iyyarsa ba su san komai ba sai maguɗin zaɓe.

James yace “Idan babu maguɗi, gwamna Ortom da jam’iyyarsa ta PDP ba zasu iya kai bantensu ba a kowane zaɓe a jahar Benuwai.”

“Wannan karon APC dai-dai take da shi, domin ba zamu sake bari ya yi maguɗin zaɓe ba a jahar Benuwai. Maganganunsa na nuna wata maƙarkashiya da ake shirya wa.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here