An Garkame Abdulrasheed Maina a Gidan Yari

 

An koma gidan jiya, kotu ta garkame AbdulRashid Maina a gidan yari.

An gurfanar da shi a kotu ne bayan taso keyarsa daga kasar Nijar ranar Alhamis.

Ana zarginsa da almundahanan kudin yan fansho sama da naira bilyan biyu.

Bayan watanni uku da bashi beli, an mayar da AbdulRashid Maina kotu da safiyar Juma’a, 4 ga watan Disamba, 2020.

An gurfanar da shi gaban Alkali Okong Abang. Alkalin ya bada umurnin garkameshi a gidan yari har sai an kammala shari’arsa.

Hakan ya biyo bayan bukatar da lauyan hukumar yaki da cin hanci da rashawa, EFCC, Mohammed Abubakar, ya gabatar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here