Kebbi: Kotu ta Bada Umarnin Garkame Matar da ta Saci Jariri

 

Kotun Majistare ta IV a Birnin Kebbi, ta bada umurnin garkame wata mata mai suna, Patricia Nebochi, a gidan yarin Argungun kan laifin satan dan jariri a jihar.

Matar, mai zama a garin Tambuwal ta saci jaririn ne a asibiti Aisha Muhammadu Buhari dake garin Jega, Daily Trust ta ruwaito.

Miss Nebochi, ta saci yaron wata mata mai suna Fatimah Galbi, yar garin Galbi, karamar hukumar Jega ta jihar Kebbi.

Lauyan yan sanda, Sifeto Muttari, ya bayyanawa kotu cewa “a ranar 21 ga Nuwamba, 21, 2020, misalin karfe 4 na yamma, wani mai gadi a asibiti ya damke matar da ta saci jaririn.”

Mai gadin mai suna Mati yace, “lokacin da ake kokarin kamata, ta jefar da jaririn don ta gudu, kuma sakamakon haka jaririn ya mutu”.

Lauyan yace ana gurfanar da ita ne kan laifi satan mutum da kisan kai.

Saboda haka ya bukaci kotu ta garkame ta a gidan kurkuku kafin hukumar yan sanda ta kammala bincike.

Alkalin kotun, Zainab Bello Suru, ta bada umurnin a tsareta a kotun yayinda ta dage karar zuwa ranar 5 ga Junairu, 2021.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here