Bayan Garkuwa: Mutane 11 Sun Gudu Daga Hannun ‘Yan Bindiga a Jahar Kaduna

 

Mutane 11 da aka yi garkuwa da su sun tsere daga sansanin ‘yan fashi bayan jami’an tsaro sun far ma miyagun.

Gwamnatin Kaduna ce ta sanar da wannan ci gaban yayin da ta ke yabawa ayyukan tsaro a jahar Samuel Aruwan, kwamishinan tsaro na ihar ya ce mutanen sun kubuta ne daga sansanin da ke wajen garin Sabon Birni a karamar hukumar Igabi Jahar.

Kaduna – Gwamnatin jahar Kaduna ta ce wasu mutane da aka yi garkuwa dasu su 11 sun tsere daga sansanin ‘yan bindiga yayin da ayyukan tsaro ke ci gaba a jahar, PM News ta ruwaito.

Mista Samuel Aruwan, Kwamishinan tsaron cikin gida da harkokin cikin gida ya tabbatar da ci gaban a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a Kaduna.

Aruwan ya ce:

“Rahotanni daga hukumomin tsaro sun sanar da gwamnatin jahar Kaduna cewa mutane 11 da aka yi garkuwa da su sun tsere daga sansanin ‘yan bindiga da ke wajen garin Sabon Birni na karamar hukumar Igabi ta jahar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here