Gwamantin Tarayya za ta Rasa Makudan Kudin da ta ke Samu Daga Harajin VAT

 

Rahotanni sun nuna kudin shigan da gwamnatin tarayya ke samu zai ragu.

Alkali ya ba gwamnatin jahar Ribas gaskiya a shari’ar ta da FIRS a kan VAT.

Gwamnatin Tarayya ta samu N2.5tr daga VAT bayan an kara harajin a 2020.

Abuja – Bisa dukkan alamu, gwamnatin tarayya za ta rasa makudan kudin da ta ke samu daga harajin VAT, game da karancin kudin shiga da ake fuskanta.

Daily Trust ta ce gwamnatin tarayya ta gamu da karin cikas a lokacin da ake kuka da tasgaron da annobar cutar COVID-19 ta kawo wajen samun kudin shiga.

Ya gwamnatin tarayya ta kare a kotu?

Hakan na zuwa ne bayan hukuncin da kotu ta yi, inda aka ba gwamnatin jihar Ribas gaskiya a karar da ta kai game da wanda ke da alhakin karbar VAT a jaha.

Lauyan gwamnatin Ribas, Donald Chika Denwigwe (SAN), ya nemi kotu ta raba gardama ko tsakanin gwamnoni da FIRS a kan inda harajin VAT zai shiga.

Lauyan da ya tsaya wa hukumar FIRS, O.C. Eyibo, ya fara nuna gwamnati za ta daukaka kara.

Jaridar ta ce mafi yawan kudin da gwamnatin tarayya ta ke samu ya na fito wa ne daga arzikin mai, yayin da gwamnoni ke raina kason da ake ba su duk wata.

A daidai lokacin da wannan hukunci zai taimaki jihohin da za su iya karbe harajin VAT na kayan masarufi sosai, wasu jahohin sun dogara ne da gwamnatin sama.

BudgIT ta ce a cikin jahohi 36 da birnin tarayya, jahohi biyar ne suka fi bada gudumuwa a asusun VAT. Legas,, Ogun da Ribas da ta kai gwamnati kotu suna cikinsu.

Naira Tiriliyan 2.5 a shekara daya da rabi

Rahoton yace bayan Muhammadu Buhari ya kara VAT zuwa 7.5% a shekarar bara, Najeriya ta samu Naira tiriliyan 2.5 tsakanin Junairun 2020 da Yunin 2021.

Alkaluman da NBS ta fitar sun nuna cewa a rabin shekara, gwamnatin tarayya ta samu fiye da Naira tiriliyan daya a 2021, wannan labari ya na daf da ya canza.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here