Anyi Garkuwa da Sakataren Hukumar Zaɓe na Jahar Nasarawa

 

Wasu yan bindiga da ba’a san su ba sun yi awon gaba da sakataren hukumar zaɓe ta jahar Nasarawa, Barista Muhammad Abubakar.

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun kai harin gidan sakataren da daren ranar Talata, kuma suka tafi daashi.

Kwamishinan yan sandan jahar Nasarawa ya ɗauki matakin gaggawa domin kubuyar da sakataren da kame maharan.

Nasarawa – Yan bindiga da ba’a san su ba sun sace sakataren hukumar zaben jahar Nasarawa (NASIEC), Barista Muhammad Abubakar, kamar yadda Punch ta rawaito.

Kakakin rundunar yan sandan jahar, ASP Rahman Nansel, shine ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Lafia, babban birnin Nasarawa.

Ya bayyana cewa maharan akalla su biyar sun farmaki gidan sakataren NASIEC, dake kauyen Bakin Rijiya, kan hanyar Lafia zuwa Shendam da misalin karfe 11:45 na daren Talata.

‘Yan bindigan sun sami nasarar awon gaba da shi zuwa wani uwri da ba’a sani ba, a cewar jawabin kakakin ‘yan sandan, kamar yadda The Nation ta rawaito.

Jawabin yace:

“Ranat 25 ga watan Agusta an shigar da kara ofishin yan sanda na Lafia cewa wasu mahara akalla 5 sun kai hari gidan sakataren NASIEC dake kauyen Bakin Rijiya, sun tafi da shi.”

Wane mataki jami’an tsaro suka ɗauka?

Kakakin yan sandan ya bayyana cewa bayan samun wannan rahoton ne kwamishinan yan sanda, CP Adesina Soyemi, ya tada tawagar jami’an yan sanda cikin gaggawa zuwa wurin da ake zargin maharan na tsare da wanda suka sace.

ASP Nansel yace an umarci mataimakin kwamishinan ‘yan sandan jahar, mai kula da sashin binciken kwakkwafi na manyan laifuka ya gudanar da bincike kan lamarin, domin kubutar da sakataren da kame maharan.

Ya yi kira ga al’ummar jahar su taimakawa jami’an tsaro da bayanai, wanda zai saukaka musu aikinsu, a kuɓutar da wanda aka sake sannan a kame maharan.

NASIEC zata gudanar da zaɓe

Hukumar NASIEC ta sanar da cewa zata gudanar da zaɓe a kananan hukumomi 13 na jahar domin cike gurbi kujerun shugabanni da kansiloli a ranar 6 ga watan Oktoba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here