Anyi Garkuwa da Wani Shugaban Cocin Katalika
Wasu da ake zaton yan bindiga ne sun yi awon gaba da wani limamin cocin Katolika a Abuja.
Rundunar yan sandan birnin tarayya ta tabbatar da lamarin wanda ya afku a ranar Lahadi.
Tuni dai jami’an tsaro suka bazama domin ceto shi tare da kama masu laifin Wani rahoto da jaridar TheCable ta wallafa ya nuna cewa yan bindiga sun yi garkuwa da wani limamin cocin Katolika a babbar birnin tarayya Abuja.
An tattaro cewa an sace limamin cocin ne a kewayen Yangoji, wani gari da ke kusa da yankin Kwali a babbar birnin tarayya, a ranar Lahadi, 22 ga watan Nuwamba.
Read Also:
Da take tabbatar da lamarin a cikin wata sanarwa a ranar Litinin, rundunar yan sandan birnin tarayya ta bayyana cewa ta kaddamar da wani aiki domin ceto limamin cocin.
Miriam Yusuf, mai magana da yawun rundunar, ta bukaci mazauna yankin birnin tarayya da su kwantar da hankalinsu sannan su kai rahoton duk wani yunkuri da basu gamsu da shi ba.
Yusuf ta bayyana cewa yan sanda a birnin tarayyar kasar sun jajirce domin kare rayuka da dukiyoyin mazauna yankin.
“Kwamishinan yan sanda na birnin tarayya, Bala Ciroma, ya kaddamar da wani farauta don ganowa tare da kama masu laifin,” in ji ta.
“Yayinda take bukatar mazauna yankin da su zamo masu lura da kai rahoton duk wani motsi da basu gamsu da shi ba a kan lokaci, rundunar na burin jaddada jajircewarta wajen kare rayuka da dukiyoyi a birnin tarayya.”
Lamarin rashin tsaro a kasar ya san gwamnati da al’umman kasar cikin damuwa.