Ranar Fara Gasar Cin Kofin Kwallon Kafa ta Afirka 2023
Ƙasar Ivory Coast za ta karɓi bakuncin gasar Cin Kofin Afrika (AFCON) na bana wanda za a fara daga 13 ga watan Janairu zuwa 11 ga watan Febrairu.
Wannan ne karo na biyu da ƙasar za ta karɓai bakuncin gasar, bayan wanda ta yi a shekarun 1984, da kuma ta kasance gasa ta 34 tun bayan kirkiro ta a 1957.
Tun da farko an shirya gudanar da gasar a watan Yuni zuwa Yulin 2023, amma sai aka ɗage ta saboda fargabar buga ta a lokacin damina.
Za a buɗe gasar ne da wasa tsakanin mai masaukin baki wato Ivory Coast da ake yi wa laƙabi da ‘Giwaye’, inda za su fafata da ɗaya daga cikin abokan karawarsu a rukunin A.
Filin wasa na Alassane Ouattara da ke Abidjan babban birnin ƙasar ne zai karɓi bakuncin wasan karshe a ranar 11 ga watan Fabrairu.
 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com