Shin da Gaske Shekarau na Shirin Komawa PDP ?

 

Sanata Ibrahim Shekarau, tsohon gwamnan Jihar Kano ya musanta rahoton cewa yana shirin fita daga jam’iyyar NNPP ya koma PDP.

Sanatan mai wakiltar Kano Central ya bayyana hakan ne ta bakin hadiminsa Malam Bello Sharada amma ya tabbatar Atiku ya yi wa Shekarau tayi sai dai kwamitin Shura ba ta amince ba.

Bello Sharada ya kuma bayyana cewa wasu daga bangaren Malam Shekarau sun yi korafin cewa Sanata Rabiu Kwankwaso bai cika musu alkawarin da ya yi na basu tikiti ba a NNPP.

Jihar Kano – Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya yi watsi da tayin da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar na komawa PDP.

Hadimin Sanata Shekarau, Malam Bello Sharada, ya fada wa Sahelian Times a ranar Talata, ya kara da cewa kwamitin Shura ta Ibrahim Shekarau ta yi amincewa da neman da PDP ke yi na sanatan da ke wakiltan Kano Central ya koma PDP.

Sharada ya kara da cewa a yayin taron da aka yi a ranar Lahadi, 14 ga watan Agusta na 2022 a gidan Shekarau na Mundubawa a Kano, an tattauna wasu muhimman abubuwa baya da tayin da Atiku Abubakar ya yi.

“Ka san cewa Malam Shekarau ya taba takarar shugaban kasa a tsohuwar jam’iyyar ANPP, hakan yasa wasu yan takarar shugaban kasa ke tuntubarsa. Kuma a wurin irin wannan tarukan ne suka hadu da Atiku kuma ya masa tayin ya koma PDP.”

Ya bayyana cewa lokacin da kwamitin shura suka zauna taro a ranar Lahadi, sun tattauna ganawar Shekarau da Atiku sanna suka yanke shawarar Shekarau ba zai karbi ‘tayin da ya masa mai gwabi ba’.

Sharada ya tabbatar da cewa wasu a bangaren Shekarau sunyi korafi

Hadimin na Shekarau ya tabbatar da cewa wasu a bangaren tsohon gwamnan na Kano sun koka kan abin da suke yi wa kallon rashin adalci da saba alkawari da Kwankwaso ya yi, rahoton Sahelian Times.

Ya tunatar cewa yayin tattaunawa da aka yi kafin sanatan ya koma NNPP, an masa alkawarin tikitinsa da na wasu magoya bayansa ba tare da hamayya ba, amma Kwankwaso bai cika alkawarin ba kawo yanzu don kawai Shekarau shi kadai ya samu tikitin.

“Ka ga, ba mu da yan takarar majalisar wakilai na tarayya, da na majalisar dokokin jiha a zaben 2023. Ba mu da wakilai a shugabancin jam’iyya, tikitin Malam Shekarau kadai Kwankwaso ya cika alkawarin hakan.”

A baya, wata jaridar kafar intanet ta rahoto cewa Shekarau ya yi mabanbanta taruka da Atiku Abubakar, da abokin takararsa Ifeanyi Okowa da shugaban PDP na kasa, Iyorchia Ayu, kan jita-jitar komawarsa PDP.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here