Cin Hanci: IGP Baba ya Karrama DPO Kan Kin Karbar $200,000

 

Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya, Alkali Baba ya karrama wani DPO a jihar Kano da lambar yabo saboda yaki karban cin hanci.

Jami’an ‘Yan sanda sun kama wani babban lauya mazaunin jihar Kano da wasu yansanda da laifin fashi da makami.

IGP alkali Baba ya da umarnin a cigaba da gudanar binciken yan fashin da aka kama a hedikwatar yansanda dake Abuja.

Abuja – Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya, IGP Usman Alkali Baba ya karrama DPO na Unguwar Nasarawa dake jihar Kano SP Daniel Itse Amah, da Satifiket din lambar yabo.Rahoton THE NATION

DPO na Unguwar Nasarawa SP Daniel, ya nuna bajinta da kwarewa a aikin sa, yayin da ya ki karba cin hancin dala USD 200,000 da aka bashi akan kamun wasu yan fashi da makami.

A wata wasika dake kunshe da karramawa, IGP ya jinjinawa SP Daneil da ya nuna kwarewa da bajinta wajen kama wani babban lauya mazaunin jihar Kano, Ali Zaki da wasu yansanda.

Rahotanni sun nuna binciken da jami’an yansanda dake karkashin SP Daniel suka gudanar ya kai ga kama kungiyar wasu yan fashi da makami a jihar Kano.

Bayan haka an mayar da shariar hedikwatar yansanda Najeriya dake Abuja bisa umarnin Sufeto Janar na yansanda dan cigaba da gudanar da bincike a boye kamar yadda Tribune Oline ta rawaito

Jami’in hulda da jama’a na rundunar yansandan Najeriya, CSP Olumuyiwa Adejobi, ya tabbatar da kamun da aka yi.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here