Gbajabiamila Zai Jagoranci Kwamiti na Musamman da ke da Alhakin Cike Gurbin Nade-Naden da Aka Rusa
Shugaban kasa Bola Tinubu ya nada shugaban ma’aikatansa, Femi Gbajabiamila, domin ya jagoranci wani kwamiti na musamman da ke da alhakin cike gurbin nada-naden da aka rusa.
Aikin kwamitin shine kafa tsarin zabar wadanda za a ba mukamai daidai da tanadin doka da cancantar wadanda za a nada a hukumomin gwamnati.
Sauran mambobin kwamitin sun hada da SGF, George Akume, mai ba shugaban kasa shawara ta musamman kan harkokin siyasa da gwamnatoci, Mallam Yau Darzo.
Abuja – Shugaban kasa Bola Tinubu ya nada shugaban ma’aikatansa, Femi Gbajabiamila, domin ya jagoranci wani kwamiti na musamman da aka daurawa alhakin cike gurbin shugabannin hukumomin gwamnatin tarayya da aka rushe.
Read Also:
Kamar yadda jaridar Nigerian Tribune ta rahoto, kwamitin da shugaban kasar ya kafa shine ke da alhakin kafa tsarin zaben wadanda za a nada a mukaman daidai da tanadin doka da cancantar wadanda za a nada a Ma’aikatu, Cibiyoyi da Hukumomin Gwamnati.
Jaridar ta ambaci wata majiya tana cewa Shugaban kasa Tinubu ya daurawa kwamitin da Gbajabiamila ke jagoranta alhakin fahimtar hukumomin wadanda dokar kafa su ta tanadi ainahin matakin karatu da sai mutum ya kai domin darewa matsayin.
Nade-naden hukumomin gwamnati: SGF George Akume, da wasu za su yi aiki tare da Gbajabiamila
Legit.ng ta tattaro cewa sauran mambobin kwamitin na musamman sun hada da sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Sanata George Akume, mai ba shugaban kasa shawara ta musamman kan harkokin siyasa da gwamnatoci, Mallam Yau Darzo da wasu masana harkokin shari’a da kamfanoni masu zaman kansu.
Ku tuna cewa a kwanaki ne shugaban kasar ya sanar da rushe shugabannin hukumomin gwamnatin tarayya, sai dai abun bai shafi wasu hukumomin ba.