Covid-19: Majalisar Dokokin Ghana za ta Binciki Yadda Aka Kashe $1.5bn Wurin Yakar Annobar
Yan majalisar dokoki a Ghana za su binciki yadda aka kashe dala biliyan daya da rabi wurin yakar annobar Corona a kasar.
Hakan ya biyo bayan samun bayanai mabambanta da ke kunshe a takardun da ministan kudi Ken Ofori-Atta ya gabatar.
Read Also:
‘Yan majalisar bangaren adawa sun ce ministan ya kasa ba da gamsasshen bayanin kan yadda aka kashe kudin, a lokacin da ya je gaban majalisar ranar Laraba.
Sai dai ministan ya ce babu nuku-nuku kan yadda gwamnati ta kashe kudaden na covid-19.
A yanzu Shugaban majalisa Alban Bagbin ya umurci kwamitocin kudi da na lafiya su binciki yadda aka kashe wannan kudi.