Ghana ta Karyata Labari da ke Cewa ta Gargaɗi ‘Yan Kasarta Kan Zuwa Najeriya
Ma’aikatar harkokin wajen Ghana ta fitar da sanarwar da ke karyata wani labari da ke cewa ta gargaɗi ‘yan kasarta kan zuwa Najeriya.
A yammacin jiya Laraba ne dai aka ga wata sanarwa a kafofin sada zumunta da ke cewa Ghana ta bukaci ‘yan kasarta su yi taka tsantsan yayin ziyartar Abujan bisa dalilai na tsaro.
Read Also:
Sanarwar tazo da bazata, duba da kyakykawar alakar da ke tsakanin kasashen na Ghana da Najeriya da kuma irin ce-ce-ku-ce da har takai ga harzuka wasu hukumomin Najeriya da makamanciyar wannan sanarwar ta yi a baya bayan nan.
Sai dai kuma da safiyar wannan Alhamis ɗin ma’aikatar harkokin ƙetaren kasar ta ce bata da masaniya kan wancan sanarwar.
Hakazalika ba ta samu wasu bayanai da ke nuna cewa Najeriya barazana ce ga ‘yan kasar ba. Sannan sun nemi afuwa kan yanayi ko tashin hankali da wannan sanarwa ta farko ta jefa matafiya.