Gidan Namun Dajin da Yafi Kyau a Afrika
Hukumar kula da tafiye-tafiye ta duniya ta bayyana gidan namun dajin Serengeti da ke Tanzania a matsayin wanda ya fi kowanne kyau a Afrika a 2021.
A 2019 da 2020 da 2021 shi ne ya zo a matsayi na uku na gidan da ya fi kowanne kyau a duniya kamar yadda hukumar namun daji ta Tanzaniya ta bayyana.
Read Also:
Sauran gidajen da aka zaba sun hada da Game Reserve Botswana, da Elosha a Namibia, Kidepo Valley da ke Uganda; Sai Kruger da ke Afrika Ta Kudu da kuma Maasai Mara na Kenya.
Akwai fadin kasa mai murabba’i 14,763, kuma ya yi kaurin suna wajen dabbobi daban-daban da ke gidan ga tsuntsaye da sauran halittu.
Akwai kimanin nau’ukan dabbobi masu shayarwa 70 da na’ukan tsuntsaye 500 a wannan gidan dabbobi.