Bikin Babbar Sallah: Gidauniyar AAG ta Tallafawa Al’ummar Nijeriya da Nijar Sama dasu 10,0000

Raguna
Raguna

A kokarinta na ganin ta tallafawa marayu,gajiyayyu,marasa karfi dama al’umma baki daya,gidauniyar Adamu Abubakar Gwarzo ta tallafawa sama da mutane dubu goma(10,000) da gudunmuwar kayan masarufi,raguna,da kuma shanu yayin bikin Sallar Babbar idi ta bana, a tsakankanin kasar Nijeriya da kuma Nijar.

Jawabin hakan ya fito ne daga bakin babban daraktan gidauniyar Dr.Musa Abdullahi Sufi a tattaunawar sa da ‘yan Jarida mai taken ” Tallafin Eid Ga Marasa Karfi a Afrika”.

Dr.Sufi ya bayyana cewar wannan wani ba’ari ne a kokarin kungiyar na saisaita hanyar cigaba da tallafawa mabukata.

Gidauniyar ta taba rayukan al’umma musamman,marayu,yan gudun hijira,da mabukata,a cikin kauyuka da birane,a inda aka bawa iyalai da dama kayan abinci da kayan masarafi,da kuma yanka shanu da raguna.

Dr.Sufi ya kara da cewar gidauniyar na kokari wajen raba kayayyakin ga mutanen da suka dace ta hanyar zakulo wanda suke cikin yanayi na bukata.

Guda daga cikin wadanda suka rabauta da tallafin Mallam Ibrahim Rijiyar Lemo a Jihar Kano, ya bayyana cewar ya fidda ran samun komai,kwatsam sai yaji an kwankwasa masa Gida,an bashi nama,kayan abinci da kuma kudi,ya bayyana jin dadinsa mara misaltuwa tare da alkawarin cigaba da yiwa Prof.Adamu Abubakar Gwarzo Addu’a shi da iyalinsa har abada.

A sansanin yan gudun hijira dake jihar Katsina kuwa,Malama Nabihat Lawai a madadin su,ta mika godiya da jinjinar ban girma ga Prof.Adamu Abubakar Gwarzo,tare da cewar basu taba zaton wannan tagomashi na alkhairi mai dumbin yawa ba,a inda ta zayyana cewar,ba shakka yaran zasuji matukar dadi mara misaltuwa,a sansanin dai, Khadija wadda ta rasa iyayenta a wani hari da ‘yan ta’adda sukai silar mutuwar iyayenta,ta samu tagomashin rabauta da keken guragu,ta nuna matsananin jin dadinta,domin kyautar tazo mata a bazata,tare da mika godiya mara misaltuwa ga Prof.Adamu Abubakar Gwarzo,domin tace keken zai taimaka mata wajen cigaba da ilimi.

Shima Mallam Ibrahim Malami mabukaci a bodar magama, ya wassafa isashshen farin cikinsa ya nuna ga yadda tallafin yazo gareshi tare da mika jinjina da yabawa ga Prof.Adamu Abubakar Gwarzo,da Addu’ar Allah ya jaddada rahama ga mahaifinsa da nisan kwana da mai amfani ga mahaifiyar sa.

A maradin Nijar kuwa,Abdourasheed Mahmouda guda daga cikin wanda suka rabauta ya bayyana cewar ba shakka a duk shekara Prof. Gwarzo kan gudanar da wannan aikin alkhairi baya mantawa dasu a matsayin su na masu karamin karfi.

A sakon ta ga Professor Gwafzo Hajiya Hussaina adduar gama lafiya da albarkar a rayuwata tayi gareshi da ahalinsa baki daya.Tace ba don wannan tallafi ba da baza ma susan an gudanar da idin bana ba.

Shugaban Gidan Marayu na ONG dake maradi a kasar Nijar Sheikh Muhammad wanda ya karba kayan tallafin a madadin su baki daya,yayi adduar fatan alkhairi ga Prof.Gwarzo tare da fatan alkhairi mafifici.

A duk lokutan azumi ko shagalin bikin Sallah,gidauniyar ta Adamu Abubakar Gwarzo kan gudanar da bada wannan tallafi ga marayu,da gajiyayyu da marasa karfi,a wani yunkuri na kyautata musu da kuma rage musu radadi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here