Gidauniyar Malam Inuwa Da Kokarinta Na Ilmantar Da Mutanen Karkara Da Rugage

Najeriya, kasa ce da Allah ya horewa dimbin arziki ta kowanne fanni.Idan aka duba arewacin kasar, Allah ya albarkace shi da arzikin noma a lokacin damuna da rani, har ila yau, makiyaya su ma na taimakawa matuka wajen bunkasar tattalin arzikin yankin da ma kasar bakidaya, ta hanyar samar da ingantaccen nama, nono, man shanu, takin gargajiya, da sauransu. Sai dai, a ‘yan tsakanin shekarun nan, yankin da aka sani da yalwar arziki, zaman lafiya da walwala, ya tsinci kansa a yanayin tashe-tashen hankula dalilin rikicin da ya faro tsakanin manoma da makiyaya, wanda daga bisani ya rikida ya koma kan mai uwa da wabi.

Kididdiga ta nuna cewa Arewacin Najeriya na yin asarar miliyoyin naira sakamakon rikicin Fulani da manoma, wanda a yanzu ya addabi yankin Arewa Maso Yamma, saboda haka akwai bukatar al’umma ta tashi haikan domin magance matsalar ta dukkan hanyar da ta kamata.

A mafi yawancin nazarce-nazarcen da masana tsaro suka yi, sun tafi a kan cewa abun da ya janyo wadannan rikice-rikice, satar mutane da kai hari kauyuka babu gaira babu dalili, shine jahilci, wato rashin ilmin addini da na boko da su Fulani da mutanan karkara ke fama da shi. Da yawa masu barna a cikinsu, ba su san Allah ba, balle su san daidai, ko akasin haka. Babu karatun addini, babu na boko, babu ilimin zamantakewa, babu tunanin mutuwa da sakamako.

A wani rahoto da gidan jaridar BBC Hausa ya tattara kuma wallafa a kafafen sadarwar zamani, an nuna wani kasurgumin dan fashin daji yana cewa shi baya jin komi a ransa don ya kashe mutum ko ya kona gari.

Babban Malamin addini musulunci da ke Jihar Kaduna, Sheikh Ahmad Mahmud Gumi, wanda ya shiga cikin dazuka ya kuma gana da wadannan yan fashi ya hakikance cewa manyan dalilan ricikin sun fi ta’allaka da rashin ilimin bambance fari da baki, masu tayar da zaune tsaye da ke rayuwa a cikin daji, ba su san inda kansu yake musu ciwo ba, babu Sallah, babu salati, saboda haka ya zama wajibi a tashi tsaye wajen ganin an koyar da su, manyansu da yaransu ilimin addini da na boko, domin su san Allah da kuma azabar da ke tattare da mutumin da yake aikata miyagun laifuka, su kuma san hakkin da ya rataya a kansu a matsayinsu na ‘yan kasa.

Ganin haka ne ya sa Gidauniyar Malam Inuwa (Malam Inuwa Foundation) da ke garin Hadejia a Jihar Jigawa, ta tashi haikan domin tsamo da irin wannan mutanen da ke fama da duhun jahilci, inda ta himmatu wajen koyar da su ilimin addini da na zamani, ba don komai ba sai don su san kansu, da kuma hakkokin da suka rataya a wuyansu a matsayinsu na ‘yan adam, kuma Musulmi.

Gidauniyar Malam Inuwa, wadda aka kafa da manufar tallafawa marayu, masu karamin karfi, koyawa matasa sana’o’i domin dogaro da kai, ilimantar da al’umma tare da wayar musu da kai, ta himmatu wajen ganin al’ummar karkara da suke fama da karancin ilmin addini, sun samu malamai da makarantu domin a koyar da su ilmummuka na kowane fanni.

A irin kokarinta na ba da gudunmawa wajen magance matsalar tsaro da ta addabi al’ummar Arewa Maso Yammacin Najeriya, tare da fatan da take da shi na kyautata rayuwar al’umma, Gidauniyar ta Malam Inuwa, ta dauki nauyin koyar da yaran Fulani hadi da iyayensu da ke rayuwa a cikin dazuka ilimin Alkur’ani mai girma har na tsawon shekara guda a Rugar Gadan Maje dake karamar hukumar Taura a jihar Jigawa.
Shirin Gidauniyar, wadda ke samun tallafi na musamman daga Shugaban Hukumar Bunkasa Fasahar Sadarwar Zamani ta Kasa, Malam Kashifu Inuwa, ya faro ne da garin Rugar Gadan Maje da ke cikin yankin karamar hukumar Taura a Jihar Jigawa, a matsayin gwaji, inda aka shafe tsawon shekara guda ana koyar da manya da yara ilimin sanin duniya da lahira.

Yayin yaye wasu daga cikin daliban da suka kammala karatu a makon da ya gabata, Malam Kashifu Inuwa, wanda ya samu wakilcin Dakta Husaini Yusuf Baba, ya yi jinjina ga Malaman da suke koyarwar, inda ya bayyana muhimmancin karantar da al’umma sakon da Allah Ta’ala ya aiko Annabi Muhammadu (SAW) na hakikanin addinin Musulunci, sanin ya kamata da kuma wanzar da adalci a tsakanin al’umma.

Har ila yau, a yayin kaddamarwar, Sarkin Taura, Alhaji Rabi’u, gami da Wakilin Hakimin Taura, Dagacin ‘Yan Yanga, Alhaji Auwalu Usman, sun yi jinjina tare da godiya da addu’ar fatan alheri ga mai girma jagoran gidauniyar, Malam Kashifu Inuwa kan kokarinsa na ilimantar da jama’arsu, a cewarsu, ilimi ne kadai zai iya saita al’umma su hau kan hanya madaidaiciya.

A tattaunawar da aka yi da wasu mazauna garin Taura sun tabbatar da cewa kafin fara wannan karatu, Fulanin wannan ruga suna yawan aikata ayyukan ta’addanci kamar sata, fashi, da raunata mutane babu gaira babu dalili, amma daga lokacin da Gidauniyar Malam Inuwa ta fara koyar da su karatu, aka samu zaman lafiya a yankin.
Fulanin wannan ruga sun nuna farin cikinsu matuka, sun kuma gamsu da cewa yanzu an san da zamansu, don ba su taba samun manyan baki da suka halarci rugarsu ba sai ta dalilin wannan shiri.

Domin wanke musu zuciya ta hanya koyar da su da ilmi, shugaban Gidauniyar ta Malam Inuwa ya yiwa Fulanin alkawarin kammala Masallacin da aka fara ginawa cikin gaggawa, tare da samar da abubuwan da kowane Masallaci yake da bukata don a gudanar da ibada, sannan za a samar musu makarantu na musamman don koyar da su ilmi.

Hakika wannan ci gaba ne mai girma wanda zai taimaka wa al’umma matuka wajen sanin Allah da kuma dakile matsalar gurbacewar tunani da ake samu a tsakanin mutanen da ke rayuwa a cikin daji da rugage,Gidauniyar Malam Inuwa ta himmatu wajen aikin hadin gwiwa da sauran gidauniyoyin samar da ci gaba domin magance matsalolin al’umma daban-daban ta hanyar aiwatar da tsare-tsaren gano matsalolin jama’a da bullo da dabarun magance su, musamman samar da walwala a tsakanin al’umma.

Gidauniya ce ta mutane masu son taimakon al’umma duba da karuwar yara marayu sanadiyyar tashe-tashen hankula da fadace-fadace da ake fama da su a yankin arewa, shi ya sa ta fito da tsaruka domin gudanar da ayyukan taimako, agaji, da jin-kai daidai da bukatar al’umma.

Gidauniyar Malam Inuwa ta himmatu kwarai wajen taimakon al’umma, domin a kwanakin baya ma ta yi hadin gwiwa da Kungiyar Matasa Musulmai ta Duniya, ‘World Assembly of Muslim Youth’ (WAMY), da Gwamnatin Jihar Jigawa, inda ta yi wa akalla mutane dubu takwas da dari bakwai da talatin (8730) aikin ido tare da raba musu gilashi kyauta, wanda ya gudana a babban asibitin Hadejia.

Haka zalika, Gidauniyar da tallafin gidauniyar Qatar ta kara shirya wani aikin gyaran idon da ba da magani da gilashi kyauta wanda jimillar mutane dubu biyu da dari da bakwai (2107) suka ci gajiyarsa a babban Asibiti da yake karamar hukumar Gumel.

Ba ta tsaya a nan ba, Gidauniyar, har ila yau, da hadin gwiwar takwararta ta Qatar, ta gabatar da shirin tallafa wa matasa maza da mata, ta hanyar koya musu sana’o’i daban-daban, tare da ba su tallafin dogaro da kai, domin sanya farin ciki a zukatansu da hana fadawa yanayin da ka iya jefa al’umma cikin tashin hankali da rashin zaman lafiya.

Gidauniyar Malam Inuwa na ci gaba da samun yabo, jinjina, da addu’ar fatan alkhairi daga al’umma bisa namijin kokarin da take yi na tallafa wa marasa karfi a fannoni da dama.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here