Gwamnatin Tarayya Zata Gina Sabon Matatar Man Fetur
An kaddamar da sabon karamar matatar man fetur a kudancin Najeriya.
Hakazalika shugaba Buhari kaddamar da ginin sabon wani matatan duk na kamfani daya.
Har yanzu ana sauraron attajiri Aliko Dangote ya kammala ginin nasa matatar dake Legas.
Shugaba Muhammadu Buhari ya halarci taron kaddamar da sabon matatar man feturin WalterSmith dake Ibigwe Oil Field, jihar Imo a ranar 24 ga Nuwamba, 2020.
Buhari ya jagoranci taron ta yanar gizo. Shugaban kasan ya ce ginin wannan sabon matatar man zai taimaka wajen samar da isasshen man feturr a kasa tare da dakatad da saya daga waje.
Read Also:
Matatar man a cewar Buhari, za ta rika tace mai ganga 500 yayinda za’a fara ginin sabo wanda zai rika tace mai gana 45,000 kulli yaumin.
“Samar da hanyar gina matatun mai zai taimaka mana wajen zama masu fitar da mai zuwa ga makwabtanmu da kuma duniya gaba daya, ” Buhari yace.
Daga cikin wadanda suka halarci taron sune gwamnan Imo, Hope Uzodinma; ministan mai, Timipre Sylva; shugaban NNPC, Mele Kyari; Sakataren NCDMB, Simbi Wabote; da shugaban kamfanin WalterSmith, Abdulrazaq Isa.
Wannan matatar mai ba mallakin gwamnatin Najeriya bane. Kamfanin WalterSmith Petroman Oil Limited ke da kashi 70% na hannun jari yayinda gwamnatin Najeriya ke da hannun jarin 30%.