Hi-Impact: Gobara ta Kona Gidan Talabijin Din Watsa Labarai na HD a Jahar Ogun

 

Wata kazamar gobara ta lashe gidan talabijin din Hi-Impact, gidan watsa labarai na HD na farko a Najeriya.

Gobarar ta fara cin ma’aikatar ne a ranar Alhamis sannan wurin watsa shirye-shiryenta ya kone kurmus.

Hukumar kashe gobarar jahar Ogun ne ta tabbatar da aukuwar lamarin a wata takarda ta ranar Juma’a.

Ogun – Wata kazamar gobara ta kone gidan talabijin din Hi-Impact, gidan watsa shirye-shiryen talabijin na HD na farko a Najeriya dake jahar Ogun.

Bangaren watsa shirye-shiryen yana harabar Hi-Impact Planet Amusements Park & Resort dake wurin kilomita 12 a titin Lagos zuwa Ibadan a Ibafo dake karamar hukumar Obafemi Owode jahar Ogun.

Daily Trust ta ruwaito cewa, gobarar ta fara ne tun ranar Alhamis kuma bangaren watsa shirye-shiryen ya cinye kone kurmus.

Hukumar kwana-kwana ta tabbatar da aukuwar lamarin

Hukumar kwana-kwanan jahar Ogun ne ta tabbatar da aukuwar lamarin a wata takardar da suka saki a ranar Juma’a.

Kamar yadda takardar wacce jami’in hulda da jama’an hukumar kwana-kwanan, Bunkunola Kuti, ya sanya hannu, ya ce an gano tushen gobarar kuma cikin hanzari ma’aikatan kwana-kwanan suka kashe wutar.

Kamar yadda takardar tazo:

Jami’an kwana-kwana dake Isheri a jahar Ogun wacce Injiniya Akinwande Abiodun yake shugabanta, sun amsa kiran da ma’aikatar yada labarai tayi.

Sannan sun tabbatar da cewa babu asarar rai ko daya, sai dai duk wasu tsadaddun kaya sun kone a wurin, Daily Trust ta wallafa.

Kwanishinan harkoki na musamman, Barista Femi Ogunbanwo da darektan hukumar kwana-kwanan jahar, Fatai Adefala ya kai ziyara a maimakon gwamnati kuma ya jajanta wa kamfanin da ma’aikatan akan mummunan al’amarin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here