Gobara ta Lalata Dukiya ta Biliyoyin Naira a Kano
Gobara ta tashi a wata kasuwar ƴan gwangwan da ke Dakata a jihar Kano ta lalata dukiya ta biliyoyn naira.
Kakakin rundunar ƴansandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da labarin inda ya ce ba a samu asarar rai ba.
Read Also:
Bayanai sun ce gobarar ta soma ne bayan da aka ga tartsatsin wuta daga wasu sandunan wutar lantarki inda kuma nan da nan ta bazu zuwa masana’antar sarrafa gyaɗa.
Kwamishinan ƴansanda na Kano, Ahmed Bakori ya kai ziyara inda lamarin ya faru inda ya bayyana yanayin a matsayin abin takaici.
Ya kuma ce an kama wani mutum da ya yi koƙarin sace wasu kayayyaki a wurin gobarar.
A cewarsa za a gudanar da bincike mai zurfi domin kare sake afkuwar haka.
Ya kuma yi yaba da hanzarin da jami’an hukumar kashe gobara da sauran mutanen gari suka yi wajen kashe wutar.