Gobara ta Lalata Wayoyin Intanet a Tsaunin Kilimanjaro
Gobarar daji da ta tashi a tsauni mafi tsawo a nahiyar Afirka wato Mount Kilimanjaro a Tanzania ta lalata wayoyin intanet da aka sanya wata uku da ya gabata.
BBC ta ga wayoyin da suka kai tsawon kilomita 4 da wutar ta lalata a mahayar tsaunin ta Marangu.
Read Also:
Har yanzu hukumomin kasar ta Tanzania ba su bayyana yawan barnar da wutar ta yi ba.
Konewar wayoyin ta haifar da cikas ga samun intanet a kan tsaunin, mai tsayin mita 5,895 ko kafa 19,341.
Gobarar ta fara ne ranar 21 ga watan Oktoba kuma wannan lokacin take tashi nan da can yayin da daruruwan ‘yan kwana-kwana ke kokarin kashe ta.
Bayan watannin da aka yi ba a yi ruwa ba a jiya da kuma yau an samu ruwan sama a tsaunin abin da ya sa aka samu saukin kashe wutar.