Gobara ta yi Sanadin Rasuwar Limami, Matarsa da Yaransa 2 a Zaria

 

Wata mummunan gobara ta yi sanadin rasuwar wani mutum mai suna Mohammadu Sani, da matarsa Raulatu da yayansa guda biyu a Zaria.

Wasu mazauna unguwar sun bayyana cewa Sani shine limamin wani masallaci da ke Buhari Street, Zaria Low Cost.

Hukumar kashe gobara na Kaduna ta tabbatar da afkuwar lamarin tana mai cewa ta yi nasarar hana wutar bazuwa makwabta amma ko da ta iso wutar ta cinye sashin gidan marigayin.

Kaduna – Hukumar kashe gobara ta jihar Kaduna ta ce wani gobara da ya faru a daren ranar Juma’a ya yi sanadin rasuwar limami, Mohammadu Sani, matarsa, Raulatu Sani, dansa Hashim Sani da yarsa Fatima Sani.

Mohammad Umar, Kwamanda a hukumar mai kula da Zaria ya sanar da hakan yayin tattaunawa da manema labarai a ranar Juma’a, PM News ta rahoto.

Umar ya ce gobarar ta faru misalin karfe 1 na dare a Layin Hajiya Maituwo Low Cost, karamar hukumar Zaria.

Ya kara da cewa an kira jami’an hukumar kashe gobarar ne bayan wutar ta cinye bangare mai yawa a gidan, Vanguard ta rahoto.

Amma, Umar ya kara da cewa jami’an hukumar sunyi nasarar takaita gobarar kada ta bazu zuwa gidajen makwabta a unguwar.

Wani mazaunin unguwar ya magantu kan yadda gobarar ta faru.

Shaidan gani da ido, Malam Safiyanu Aliyu ya shaidawa NAN cewa marigayi Sani shine limamin wani masallaci da ke Buhari Street, Low Cost Zaria.

Aliyu, wanda bai fadi sanadin gobarar ba ya ce sun samu kiran neman dauki ne daga mambobin kungiyar bijilante da ke kula da unguwar.

Ya kara da cewa a lokacin da suka taho yin taimako, sun gano cewa wutar ta riga ta kona sashi gidan da marigayin da iyalansa ke zaune.

Ya ce an dauki gawar wadanda suka rasun an kai gidan iyalansu da ke Dogarawa a Sabon Gari don musu jana’isa bisa tsarin addinin musulunci.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here