Gobara ta yi Sanadiyyar Raunata Jam’an Kwana-Kwana Uku a Jahar Kaduna
Wata gobara da ta tashi a jahar Kaduna ta yi sanadiyyar raunata jami’an kwana-kwana uku.
An ruwaito cewa, wasu mutane dake kokarin kare dukiyoyinsu su ma sun jikkata a wurin.
Tuni hukumar kashe gobara ta kashe wutar ta kuma dauki jami’anta uku zuwa asibiti An samu firgici lokacin da ‘yan kwana-kwana uku da wasu mazauna gari suka samu raunuka sakamakon wata gobara da ta tashi a jahar Kaduna.
An tattaro cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 7 na safe a yankin Bushara da ke kan babbar hanyar Nnamdi Azikwe ranar Talata a wani garejin tanka da ke kusa.
An samu labarin cewa wutar ta dauki tsawon awanni uku kafin daga karshe jami’an hukumar kashe gobara ta jahar suka kashe ta.
Read Also:
Cikakkun bayanai game da tashin gobarar na ci gaba da zama a harde saboda tankunan da ke kone kurmus ciki har da wasu kalilan din shagunan kusa da garejin.
Wakilin Daily Trust da ya ziyarci wurin a ranar Laraba ya ruwaito cewa an ga mutane a gungu-gungu suna tattauna faruwar bala’in.
Wani ma’aikacin kabu-kabu da bai ambaci sunansa ba ya shaida cewa mutane da yawa sun samu raunuka yayin da suke kokarin cire motocinsu daga garejin.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jahar, Nathaniel Gaya, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce uku daga cikin mutanensu na daga cikin wadanda suka jikkata.
A cewarsa, an garzaya da jami’an uku zuwa asibiti.
Ya ce har yanzu ba a san musabbabin tashin gobarar ba amma ya bayyana cewa ma’aikatan da suka jikkata na kwance a asibiti.