Gobara ta Tashi a Harabar Cibiyar Horar da Lauyoyi ta Najeriya
An samu tashin gobara a daren ranar Laraba, 16 ga watan Fabrairu, a harabar cibiyar horar da lauyoyi ta Nigerian Law School dake kan titin Ozumba Mbadiwe a Victoria Island da ke jahar Legas.
Majiyoyin da suka zanta da ‘yan jarida sun bayyana cewa, lamarin ya haifar da tarzoma da tashin hankali a yankin.
TheCable ta ruwaito cewa, an nakalto daga majiya mai tushe a ranar Alhamis, 17 ga watan Fabrairu cewa gobarar ta tashi ne a sakamakon matsalar wutar lantarki da aka samu a cibiyar.
Read Also:
Duk da haka, an kashe gobarar cikin kankanin lokaci.
Majiyar ta ce:
“An samu tashin gobara jiya da daddare, amma nan take aka shawo kan ta. Gobarar ta faru ne sakamakon lalacewar wutar lantarki.”
A cewar Vanguard, kimanin mutane biyar da gobarar ta shafa sun kwanta a asibiti a halin yanzu.
Rahoton ya ce:
“Gobarar ta zo da wani kara. An samu turmutsutsu a dakin kwanan dalibai. Na ga wani dalibin da ya yi tsalle daga bene na farko inda gobarar ta tashi kusa da dakin karatu. Wasu daliban sun fice daga dakunansu a firgice.
“Akalla, mutane biyar sun samu munanan raunuka yayin da wata tsohuwa mace mai aikin shara ta samu gurdewa a yatsar kafa.”